1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan damben Rasha za su kaurace wa gasar Olympics

July 6, 2024

'Yan wasan damben Wrestling na Rasha sun yi watsi da tayin shiga gasar Olympics ta bana da zai gudana a birnin Paris na kasar Faransa.

https://p.dw.com/p/4hxpc
Hoto: Takuya Matsumoto/AP Photo/picture alliance

Bayan da aka haramta wa 'yan wasan Rasha shiga gasar sakamakon mamayar da Moscow ta kaddamar a Ukraine, a yanzu kwamitin shirya wasannin Olympic IOC ya bada dama ga wasu 'yan wasan kasar su fafata a gasar idan suka cika wasu tsattsauran ka'idoji da aka dauka, sai dai kuma 'yan wasan 10 da suka cike matakan su yi watsi da gayyatar.

Karin bayani: Zafi na barazana ga gasar Olympics a Paris 

Hukumar ta ce, ba su amince da wasu ka'idoji na son rai ba da kwamittin ya gindaya ba, wajen zaben 'yan wasan da suka cancanta, inda a cewarta hakan ka iya raba kawunan 'yan wasanta.

'Yan wasan Rasha da ke fatan karawa a Olympics na bana da zai gudana a birnin Paris a bazarar bana, sai sun fito karara sun nisanta kansu da mamayar da Rasha ta kaddamar a Ukraine da kuma bayyana rashin alakarsu da dakarun kasar. Rasha dai ta yi sha yin watsi da manufar IOC.