1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zafi na barazana ga gasar Olympics a Paris

Abdullahi Tanko Bala
June 18, 2024

Wani rahoto da ya sami goyon bayan masana kimiyya da yan wasan motsa jiki ya yi gargadin cewa tsananin zafi a Paris na iya yin barazana ga gasar Olympics na 2024

https://p.dw.com/p/4hCoq
Paris: Gasar wasannin Olympics na 2024
Paris: Gasar wasannin Olympics na 2024Hoto: Pascal Le Segretain/Getty Images

Wani sabon rahoto da aka fitar ya yi gargadi game da hadarin da tsananin zafi a Paris zai iya yi ga gasar wasannin Olympics  na bana.

Rahoton ya ce gasar wasannin Olympics din na Paris a yanzu yana fuskantar kalubale musamman tsananin zafi da harkar kiwon lafiya da kuma bukatar nishadantar da ma'abota wasanni da ke karuwa.

Rahoton ya ji ra'ayoyin masana kimiyya da kuma yan wasan motsa jiki.