1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan bindiga sun kashe sojoji a yankin Tillaberi na Nijar

May 23, 2024

Wasu mayakan tarzoma sun yi sanadiyyar mutuwar sojoji da ma wani farar hula a Jamhuriyar Nijar. Al'amarin ya faru ne bayan wani makamancinsa da ya faru cikin wannan mako.

https://p.dw.com/p/4gCzA
Sojojin gwamnatin Nijar
Sojojin gwamnatin NijarHoto: I. Sanogo/AFP/Getty Images

Akalla sojojin Jamhuriyar Nijar biyu da ma wani farar hula ne rahotanni ke tabbatar da cewa sun rasa rayukansu, a wani sabon hari da wasu da ake zargin mayaka masu da'awar jihadi ne suka kai yankin Tillaberi mai fama da hare-hare.

Hari ne dai da wasu dauke da makamai da ke bisa babura 20 suka kai kauyen Tabala, mai nisan kilomita 100 gabas da Yamai babban birnin kasar, kamar yadda sanarwar da ta fito daga mahukunta ke tabbatarwa.

Bayanai dai na cewa an samu gawarwakin su ma maharan akalla mutum uku, yayin da hukumomi ke cewa ana ci gaba da neman 'yan bindigar.

Wannan ne dai karo na biyu da ake kai hari kamancin wannan da aka kai a jiya Laraba a yankin na Tillaberi, bayan kisan kimanim mutum 20 a farkon wannan makon.