1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan bindiga sun halaka limami a Batsari

Mouhamadou Awal Balarabe
July 30, 2020

Wani limamin addinin Musulunci ya rasa ransa a harin da 'yan bindiga suka kai Batsari ta jihar Katsina ta arewacin Najeriya. Sai dai rundunar 'yan sanda ta jihar ba ta yi karin haske kan musabbabin harin ba.

https://p.dw.com/p/3gBG4
Karte Nigeria mit Abuja und dem Bundesstaat Katsina

'Wasu ‘yan bindiga sun halaka malamin addinin Musulunci da wani farar hula daya a karamar hukumar Batsari da ke jihar Katsina a yankin Arewa maso yammacin Najeriya. Wannan harin da ya salwantar da ran limamin Jumma'a  Malam Tukur ya faru ne cikin daren Laraba zuwa wannan Alhamis inda maharan suka bude wa limanan wuta bayan da suka afka masa, kamar yadda wani mazaunin yankin ya shaida wa wakilin DW Yusuf Ibrahim Jargaba 

Hare-hare da sace-sacen mutane don neman kudin fansa na neman zama ruwa dare a yankin na Batsari da kewaye tun bayan tabarbarewar harkar tsaro a Zamfara da katsina. Sai da a lokacin da DW ta tintibi kakakin rundunar 'yan sandan jihar Katsina SP Isa Gambo don jin matakin da aka dauka, ya ce shi ma zai tuntubi baturen 'yan sandan yankin dan jin abun da ya faru kafin yayi Karin haske.