1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ranar yaki da cin hanci ta duniya

December 9, 2022

9 ga watan Disambar ko-wace shekara rana ce da MDD ta ware domin tunatar da bukatar ci gaba da fafutukar kawar da cin hanci a tsakanin al'umma.

https://p.dw.com/p/4KkLG
Kudaden kasashe daban daban
Kudaden kasashe daban dabanHoto: Antonio Pisacreta/ROPI/picture-alliance

Yanzu haka dai Matsalar cin hanci da rashawa ta zama ruwan dare gama duniya a tarayyar Najeriya inda kusan ko-wane fanni ana samun matsalar duk da hukumomi na yaki da cin hanci da ake su da kuma matakai na yaki da cin ha ncin da gwamnatin ke ikirarin yi.

Ana ganin wannan matsala ta cin hanci da Rashawa ita ce tushen koma bayan al'amura da ake samu a kasar da su ka hana ta ci gaba.

 Kudin CFA Francs
Kudin CFA FrancsHoto: SEYLLOU/AFP

Gwamnatin Najeriya dai ta samar da hukumomi na tabbatar da yaki da cin hanci amma duk da kokarin da su ke yi ba ga raguwar cin hanci ba wanda ake ganin ana fito da sabbin Salon a wawure kudade daga lalitar gwamnati. 

Wannan ma kuma shi ne tuanin Malam Usman Abubakar mai sharhi akn al'amuran yau da kullum a Najeriya.

To sai dai akwai masu ganin matukar ba a dauki tsaurara matakai na hukunta wadan da aka samu da laifin cin hanci da Rashawa baa kwai wuya a iya magance ta tsakanin al'ummar kasar.

 Naira
NairaHoto: Ubale Musa/DW

Yanzu haka dai da 'yan Najeriya na samun shakku kan shirin yaki da cin hanci na gwamnati inda wasu ke ganin wasu tsiraru ake tuhuma yayin da ake kau da kai daga wasu da ake ganin suna kusa da gwamnati ko kuma shaffafu ne da mai.