1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Afirka da wasu sassan duniya na fama da karancin ruwan sha

October 10, 2024

Masana harkokin samar ruwan sha ta hanyar amfani da tashoshin wutar lantarki, sun ce matsalar fari na haifar da koma baya wajen samar da ruwan sha a kasashen Afirka da ma wasu na kudancin Amurka.

https://p.dw.com/p/4lcsb
Halin karancin ruwan sha a kasar Habasha
Halin karancin ruwan sha a kasar HabashaHoto: Seyoum Getu/DW

Kaso 80 cikin 100 na galibin kasashen Afirka dai sun dogara ne da ruwan sha da ake samarwa ta tashoshin wutar lantarki musamman a Jamhuriyar Dimukradiyyar Kwango da Habasha da Malawi da Mozambique da Yuganda har ma da kasar Zambiya, kasashen da ke kokarin murmurewa daga fari. Baya ga kasashen Afirka akwai kasashe kudancin Amurka irin su Colombia da Ecuador da ke  fama da tasirin fari wajen samar da albarkatun ruwan sha ta tashoshin wutar lantarki.

Babban abin da ya rage wa wadannan kasashe shi ne fadada bincike kan wasu bangarorin irin su iska da harken rana wato solar da ke iya kasancewa mafita ga kalubalen makamashi. Ghana da Kenya na daga cikin kasashen da ke kan gaba wajen kokarin inganta hanyoyi da kuma samar da sabbin matakai na zamani wajen magance wannan matsalar a cewar Giacomo Falchetta wani kwararren mai bincike kan cibiyar makamashi a kasashen Turai da Afirka.

Gina kananan madatsun ruwa da cibiyoyin sarrafa ruwan sha a gundumomi zai taimaka matuka wajen rage karfin juyawar ruwa a manyan madatsun ruwa da ke Afirka da ke haifar da ambaliyar ruwa a wasu lokutan kamar yadda ya faru a birnin Maiduguri na jihar Borno a Najeriya.

Hukumar da ke kula da makamashi ta Duniya ya hasashen cewa daga nan  zuwa shekara ta 2030, za a koma dogaro da iskar da ke kadawa da hasken rana wajen samar da makamashi da hakan zai rage dogaro da tashoshin wutar lantarki, duk da cewa hukumar ta IEA ta ce akwai jan aiki a gaban gwamnatoci wajen cimma wannan manufa a kasashen nahiyar Afirka da kudancin Amurka.