1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

AU za ta tattauna takaddamar madatsar ruwan Nilu

Mohammad Nasiru Awal SB
July 20, 2020

A wannan Talata 21 ga watan Yuli shugabannin kasashen kungiyar AU za su tattauna kan takaddamar madatsar ruwan Nilu da Habasha ke ginawa.

https://p.dw.com/p/3fcFI
Äthiopien Grand Renaissance Damm
Hoto: Reuters/t. Negeri

Fadar shugaban kasar Afirka ta Kudu ta ce a ranar Talata 21 ga wannan wata na Yuli ake sa rai shugabannin kasashen Afirka za su yi wani taron koli, inda za su tattauna kan batun madatsar ruwan nan ta Kogin Nilu da ta janyo tsamin dangantaka tsakanin Masar da Habasha da kuma Sudan.

Kungiyar tarayyar Afirka AU da yanzu ke karkashin shugabancin Shugaba Cyril Ramaphosa na Afirka ta Kudu za ta shirya taron.

Mai magana da yawun Shugaba Ramaphosa ta ce ofishin majalisar shugabannin AU da na gwamnatoci za su gudanar da taron ta hanyar na'urar bidiyo.

Madatsar ruwan da kasar Habasha ke ginawa ta janyo kace-nace tun bayan da ta fara aikin a shekarar 2011. Kasashen Sudan da Masar na ganin madatsar ruwan a matsayin barazana ga ruwan al'umominsu, yayin da ita kuwa Habasha take cewa muhimmin abu ne ga bunkasa hasken wutar lantarki da kuma ci-gaban kasar.