WHO: Gargadi kan gurguncewar tsarin kiwon lafiya a Gaza
November 11, 2023Tedros Ghebreyesus ya yi wannan gargadi ne yayin da yake gabatar da rahoto a gaban kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya inda ya ce al'amarin da ke a zahiri a Gaza ya wuce misali.
Karin bayani: Hukumomi a Gaza sun ce wasu hare-haren Isra'ila sun fada kan asibitoci guda uku a juma'ar nan
A rahoton nasa, Tedros Ghebreyesus ya kara da cewa an kai wa asibitoci da dakunan shan magani a Gaza fiye da hare-hare 250, sannan kuma lunguna da sako na asibitocin zirin sun cika sun batse da wadanda suka jikkata baya ga cinkoson gawarwaki, sannan kuma yanayin aiki ba a magana in ji shi.
Karin bayani: Asibitoci da dama sun rufe a Zirin Gaza
Shugaban hukumar lafiyar ta duniya ya kuma yi kira da a sauya fasalin kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya duba da yadda ya gaza magana da murya daya domin daukar matakin kawo karshen wannan munmunan al'amari da ke faruwa a dan karamin yankin na Falasdinu.
Karin bayani: Shugaban Amurka Joe Biden ya ce babu yiwuwar tsagaita wuta a Gaza