1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hukumomin Gaza sun ce Isra'ila ta kai hari asibitoci uku

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
November 10, 2023

Shugaban Amurka Joe Biden ya ce Isra'ilar za ta rinka tsagaita wuta tsawon sa'o'i 4 a kullum har zuwa kwanaki uku, don bai wa fararen hula damar ficewa daga arewacin Gaza da rikicin ya fi kamari, domin komawa kudanci

https://p.dw.com/p/4YeKq
Hoto: Maxppp Wissam Nassar/dpa/picture-alliance

Hukumomi a Gaza sun ce wasu hare-haren Isra'ila sun fada kan asibitoci guda uku a juma'ar nan, tare da kara tagayyara harkokin kula da dubban marasa lafiya da rikicin ya ritsa da su.

Mai magana da yawun ma'aikatar lafiyar yankin Gaza Ashraf Al-Qidra, ya shaidawa gidan talabijin na Al Jazeera cewa daga cikin asbitocin da harin ya shafa har da babban asibitin Gaza wato Al Shifa, ko da yake bai bayar da adadin wadanda suka mutu da kuma wadanda suka jikkata sanadiyyar harin ba.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya rawaito cewa har zuwa wannan lokaci Isra'ila ba ta mayar da martani kan wannan sanarwa ta ma'aikatar lafiyar Gazan ba.

Karin bayaniNeman tsagaita wuta saboda agaji:

Shugaban Amurka Joe Biden ya ce Isra'ilar za ta rinka tsagaita wuta tsawon sa'o'i 4 a kullum har zuwa kwanaki uku, don bai wa fararen hula damar ficewa daga arewacin Gaza da rikicin ya fi kamari, domin komawa kudanci.

A gefe guda kuma sojin Isra'ilan sun kai hari Syria kan wata kungiya da take zargi da kitsa harin jirgi marar matuki a wata makaranta da ke kudancin Isra'ilan a ranar Alhamis.

Karin bayani:Shugaban Amurka Joe Biden ya ce babu yiwuwar tsagaita wuta a Gaza.Biden

Wannan na cikin wata sanarwa da rundunar sojin ta wallafa yau a shafinta na X, da a baya aka fi sani da Tiwita.

A Alhamis din dai kungiyar 'yan tawayen Yemen ta Houthi mai samun goyon bayan Iran, ta yi ikirarin kai hari kudancin Isra'ila, inda ita kuma Isra'ilan ta bayyana cewa ta samu nasarar kakkabo wasu rokoki da aka harba mata.