Najeriya za ta yi ramuwa kan wasu kasashe
July 30, 2020Duk da cewar dai Najeriyar ta yi nasarar kwashe 'yan kasarta sama da 6,000 cikin tsarin kwashe 'yan kasar da COVID-19 ta janyo makalewarsu a kasashen duniya da dama, Tarayyar Najeriyar tana shirin kwasar 'yan kallo da wasu kasashe na duniya bisa batun. Kuma kama daga Kanada ya zuwa kasar Birtaniyan da ta yi wa Najeriyar mulkin mallaka dai, ana yamutsa gashin baki sakamakon matakin hana jirgin Najeriyar na Air Peace kwashe 'yan kasar da ke wadannan kasashen biyu, duk da jeri na yarjeniyoyin sufurin da ke tsakaninsu da Najeriyar.
Abun kuma daga dukkan alamu ya bata rai na al'ummar Najeriyar da ke masa kallon cin zarafi ga kasarsu. Kyaftin Bala Jibril dai na zaman mai sharhi a cikin harkokin sufurin na sama, da kuma ya ce matakin kasashen na kama da halin zamba.
Kau da kai cikin halin matsatsi ko kuma ma kokari na zamba ta aminci dai, jirage da yawa na kasashen na shiga cikin shirin kwashe 'yan kasarsu daga Najeriyar. Kuma a tunanin Kyaftin Mohammed Joji da ke zaman tsohon shugaban kamfanin jirgin saman Tarayyar Najeriyar na Nigeria Airways, akwai bukatar aiken sako a bangaren mahukuntan Najeriyar da nufin kaucewa cin mutunci ga kasarsu.
Akwai dai tsoron rikidewar rikicin daga rikicin jiragen sama ya zuwa rikicin diplomasiyya mai tsohon tarihi. Alal misali dai Birtaniyyar da ta yi wa Najeriyar mulkin mallaka da kuma ke kallon kasar a matsayin guda a cikin manyan da ke fadi a ji a kungiyar rainon Ingila da ke da dogon tarihi. To sai dai kuma a fadar ministan sufurin jiragen saman Najeriyar, Hadi Sirika ba hujjar rikicin diplomasiyya a cikin tsarin da ke da amsar dokar. Abun jira a gani dai na zaman yadda take shirin kayawa ga manyan kasashen guda biyu, da ke kallon rikidewa ta kawance sakamakon annobar COVID-19 da tasirinta ke kara mamaye bangarpri da dama na rayuwar al'umma.