Labarin Wasanni: Wa zai dauki kofin AFCON?
February 5, 2024Bayan kammala wasannin kusa da na kusa da na karshe a gasar cin kofin kasashen Afirka ta 2023 AFCON, Najeriya za ta kara da kasar Afirka ta Kudu yayin da mai masaukin baki ta Cote d'Ivoire za ta kece raini da Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango a wasannin kusa da na karshe.
A wasannin Bundesliga da ke gudana a Jamus kuwa, ga yadda wasannin suka gudana a karshen mako tsakanin kungiyoyin:
Heidenheim 0 Dortmund 0
Bayern 3 Monchengladbach 1
Freiburg 1 Stuttgart 3
Mainz 0 Bremen 1
Bochum 1 Augsburg 1
FC Kolon 2 Eintracht 0
Darmstadt 0 Bayer Leverkusen 2
A gasar Premier League ta Ingila kuwa, kungiyar Manchester United ta doke West Ham da ci uku da nema, ita kuma Burnley da FC Fulham sun tashi canjaras biyu da biyu, yayin da Arsenal ta doke Liverpool da ci uku da daya.
Faransa ta samu nasarar wauce matakin rukuni a gasar neman cin kofin Davis ta Tennis bayan doke Taiwan. Haka kasashen Sabiya da Netherlands da Finland da Jamus da Brazil da Amurka da Kanada suna cikin wadanda suka tsallaka.
Tsohon shahararren dan wasan Zari-Ruga na Wales Barry John tsohon shahararren dan wasan Zari-Ruga na Wales, ya rigamu gidan gaskiya. Marigayin da ake kiransa da sunan sarki lokacin da yake ganiyarsa a wasan na Zari-Ruga, ya bar duniya yana da shekaru 79 bayan ya sha fama da rashin lafiya.