Tsaurara tsaro a Arewa maso Gabashin Najeriya
May 2, 2018Matakin dai ya biyo bayan wasu tagwayen hare-haren kunar bakin wake da aka kai a garin Mubi na jihar Adamawa da ke yankin na Arewa maso Gabashin Najeriya ranar Talatar wannan mako da muke ciki. Masu bayar da agajin gaggawa dai sun ruwaito cewa akalla mutane 20 ne suka rasa rayukansu a harin na garin Mubi, sai dai mazauna yankin sun bayyana cewa sun binne sama da mutane 60 da suka rasa rayukansu sakamakon harin.
Harin dai na zuwa ne kwana guda bayan da shugaban Amirka Donald Trump yayin wata ganawa da shugaban Najeriyar Muhammadu Buhari wanda ya ziyarce shi a birnin Washington DC, ya alkawaranta karin taimako ga Najeriyar a yakin da take da mayakan Boko Haram, wadanda suka hallaka mutane da dama tun bayan fara kai hare-harensu a shekara ta 2009. Tuni dai mahukuntan Najeriyar ta bakin mataimakin shugaban kasar Yemi Osinbajo suka nuna takaicinsu dangane da harin.