1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaArewacin Amurka

Trump ya yi alkawarin kawo karshen rigingimun kasa da kasa

Zainab Mohammed Abubakar
July 19, 2024

Kasa da mako guda bayan da wani dan-bindiga ya yi yunkurin kashe shi yayin yakin neman zabe a jihar Pennselvania, Trump ya nemi hadin kan Amurkawa.

https://p.dw.com/p/4iUnj
Donald TrumpHoto: Mike Segar/REUTERS

Donald Trump ya amince da zabensa a matsayin dan takarar shugaban Amurka na  jam'iyyar Republican a hukumace, a yayin jawabin da ya gabatar a babban taron jam'iyyar kwanaki kalilan bayan ya tsallake rijiya da baya a wani yunkuri na hallaka shi.

Cikin jawabin na sa tsohon shugaban na Amurkan Trump ya sake jaddada bukatar magance rashin jituwa da rarrabuwar kawuna a tsakanin  al'ummar Amurkan.

Ya kara da cewa "Ina neman zama shugaban kasa gadaukacin Amurka, ba rabin Amurka ba, domin babu wata nasara da za a samu na lashe rabin Amurka."

A cikin jawabinsa na mintuna 90, wanda shi ne kololuwar taron jam'iyyar Republikan na kwanaki hudu,Trumpya yi alkawura daban-daban ga masu kada kuri'u ciki har da kawo karshen rikice-rikicen kasa da kasa, da aiwatar da aikin korar baki mafi girma a tarihin Amurka.