1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Shugabannin duniya sun yi tir da harin da aka kai wa Trump

Binta Aliyu Zurmi
July 14, 2024

Shugabannin kasashen duniya na ci gaba da mika sakon jaje ga tsahon shugaban Amirka Donald Trump bayan da wani matashi ya yi yunkunrin kashe shi ta hanyar harbi da bindiga.

https://p.dw.com/p/4iHQg
USA Butler | Schüsse bei Auftritt von Donald Trump
Hoto: REUTERS

Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya bayyana harin a matsayin barazaga ga ci gaban dimukradiyya.

Firaministan Birtaniya Keir Starmer ya ce rigingimun siyasa ta kowace siga ba su da mazauni a tsakanin al'ummar wannan karni.

Shugaba Emmanuel Macron na Faransa da ya bayyana harin a matsayin wani bala'i ga dimukradiyya, ya yi wa Trump fatan samun sauki cikin gagawa.

Shi ma a na shi sakon firaministan Canada Justin Trudeau ya ce wannan laifi ne babba da ba za a iya bayyana girmansa ba, kuma ba za a taba lamuntar irin wannan mugun al'amarin ba.

Karin Bayani: FBI ta tabbatar da yunkurin halaka Trump

Fumio Kishida firaministan Japan ya ce dole ne sai duniya ta tashi tsaye a matsayin tsintsiya daya domin yakar duk wata barazana da dimukradiyya ke fuskanta.