Trump ya ce Amurka za ta mallaki Gaza
February 10, 2025Talla
Trump ya kara da cewar wasu kasashen da ke yankin Gabas ta Tsakiya za a ba su wani sashe na Zirin domin sake gina shi.
A karon farko shugaban na Amurka zai gana da sarki Abdallah II na kasar Jordan wanda ya gayyace shi fadar White House.
Dama a baya Trump ya ce kasashen Jordan da Masar su kwashe Falasdinawa sai dai wata majiya daga fadar Sarki Abdullah ta ce basaraken ba zai amince da batun kwashe Falasdinawa daga mahaifarsu ba.
Karin Bayani: Martani kan barazanar Trump na kwace iko da Gaza