Martani kan barazanar Trump na kwace Iko da Gaza.
February 5, 2025A wani mataki da ake dauka a matsayin sauyi mafi girma game da manufofin Amurka kan rikicin yankin gabas ta tsakiya cikin gomman shekaru,da Amurkan ke daukar kafuwar kasar Falasdinu a matsayin maganinsa na warkam, shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da yanke shawarar kwace iko da zirin Gaza don mayar da shi cibiyar samun makudan kudade. Ya bayyana hakan ne a taron manema labarai a fadar White House tare da firaiministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu.
"Amurka za ta ƙarbi iko da zirin Gaza don ta zama mallakinta. Za kuma ta sake masa fasali, bayan share baraguzai da nakiyoyin da aka daddasa. Za ta gina katafaren birnin kasuwanci a zirin da zai samar da dumbin ayyuka ga mazauna yankin. Za kuma mu mayar da mazauna yankin kasashen Masar da Jodan da gina musu kyakkywa kuma yalwataccen wurin zaman da zasu zauna cikin kwanciyar hankali da nutsuwa, a madadin a sake gina musu zirin Gaza rikici ya sake ballewa tsakaninsu da Israila a sake rusata a koma gidan jiya".
Shugaban Amurkar ya kuma bayyana abin da yake tunani game da makomar gabar yamma da kogin Jordan, inda ya ce yana tunanin nuna goyon bayansa ga shirin Isra'ila na kwace iko da gabar yamma din. Nan da nan firaiministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu ya nuna jin dadinsa da kalaman na Mr Trump, inda ya ce hakan zai canza tarihi.
"Shugaba Trump na da hange na daban da ya sabawa kowa dangane da wannan dan kankanin zirin da ya addabi duniya. Domin ya zama wata kafa ta ta'addanci da fituntunu da tayar da hankulan Isra'ila dama yankin.Wannan shawarar ta yi matukar birge ni. Ina fata abokan aikinsa da sauran shuwagabannin duniya za su yi na'am da wannan shawarar wacce aiwatar da ita zai canza tarihi."
Saudiyya,wacce shugaban Amurka Trump da Natenyahun suka jima suna zarwanci ta kulla hulda da Isra,ila, wacce kuma ta tsaya kai da fata kan cewa, ba za ta yi hakan ba,sai ranar da Amurkan da Isra'ila suka shelanta kafuwar kasar Falalsdinu, ta mayar da martani cikin gaggawa kan ƙudurin Trump na shirin ƙwace iko da zirin Gaza, inda ta yi watsi da duk wani yunƙuri na raba Falasdinawa da ƙasarsu.
Kakakin hukumar Falasdinawa,Bilal Fady ya nuna takaicinsa ga yadda shugaban na Amurka ke kokarin mayar da batun kasar Falalsdinu tamkar wata jingar kasuwanci:
Akwai batutuwa da dama da shugaba Trump ke nuna rashin dattaku a kansu, ya mayar da su tsagwaron kasuwanci. Muna kara jaddada masa cewa, idan kudinsa zai iya sayen duniya, to ba zai iya sayen mutuncinmu da rayukan dubban 'yan uwanmu da suka kwanta dama kan kare kasarmu, ta hanyar aiwatar da wannan jingar tasa da ake wa lakabi da Katafariyar Gabas Ta Tsakiya bisa tsarin Amurka ba
Shi kuwa kakakin Hamas,Ahmad Daowud da ya bayyana matakin da na neman tada zaune tsaye a yankin ya kara da nuna al'ajabinsa ne ga yadda Trump ya tsaya kai da fata don korar baki da yake kiransu 'yan mamaya daga kasarsa, kana yake zaton Falalsdinawa ba za su yi duk abun da ya kamata don korar bakin da suka mamaye musu kasa suke gasa musu aya a hannu ba:
Muna nan daram a zirin Gaza. Ba inda za mu je.Bama kaunar kowa ya gina mana gidajenmu.A barmu haka mu ci gaba da zama a baraguzanmu.
Tun kafin hakan dai, Ƙasashen Masar da Jordan sun futo karara sun yi fatali da kiraye kirayen da Trump din yayi ta musu na amincewa da tsugunar da Falasdinawa a ƙasashensu.Yadda aka jiyo shugaba Al Sisi na Masar na cewa:
Tilasta wa Falalsdinawa kaura daga kasarsu zuwa wata kasar, bayan gangancin ragargaza kasarsu,zalunci ne da ba za a yi shi damu ba.
Haka nan itama Tarayyar Turai ta ce ba ta goyan bayan duk wani matakin da zai yi barazanar ga kafuwar kasar Falasdinu mai makwabtaka da Isra'ila,kudirin da Majalisar Dinkin Duniya ta kwashe shekaru ta na jajircewa kansa.