Trump ya bai wa Hamas wa'adin sakin Isra'ilawa da ke Gaza
February 11, 2025Shugaban Amurka Donald Trump ya bai wa kungiyar Hamas ta zirin Gaza wa'adin sakin dukkan Isra'ilawa da suka saura a hannunta ko kuma ta fuskanci mummunan al'amari.
Trump ya yi kalaman nasa ne biyo bayan sanar da dakatar da yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma da Hamas ta sanar a ranar Litinin.
Mista Trump ya ce daga yanzu zuwa karfe sha biyu na ranar Asabar idan ba a saki dukkan fursunonin yakin da ke hannun Hamas ba to za a fada mummunan yanayi.
Netanyahu zai gana da Trump kan yakin Gaza
Ko da yake Trump ya kara da cewa maganar ta kashin kansa ce, saboda daukar mataki na wuyan Isra'ila wacce ya ce matakin nata ka iya zama daban da kalamansa.
Gaza: Trump ya bukaci Masar da Jordan su karbi Falasdinawa
Dama an tsara sako karin wasu Isra'ilawa uku a ranar Asabar mai zuwa kafun sanarwar ta Hamas inda ta ce Isra'ila ta karya ka'idar yarjejeniyar.