1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tinubu ya nada shugabannin leken asiri

Usman Shehu Usman
August 26, 2024

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya nada sabbin shugabannin lekern asirin kasar wato hukumar leken asirin al'amuran wajen Najeriya (NIA) da kuma hukumar 'yansandan farin kaya ta (DSS)

https://p.dw.com/p/4jwaZ
Nigeria | Bola Tinubu
Hoto: Sunday Aghaeze/Nigeria State House via AP/picture alliance

Wata sanarwar da ofishin kakakin fadar shugaban kasar ya raba wa manema labarai ta bayyana cewa, Tinubu ya nada Ambassador Mohammed Mohammed a matsayin babban daraktan hukumar kula da leken asirin al'amuran wajen kasar da aka sani da NIA haka kuma Tinubu ya nada Mr. Adeola Oluwatosin Ajayi a matsayin shugaban hukumar 'yan sandan farin kaya da aka sani DSS. Sanarwar ta kara da cewa Ambassador Mohammed ya yi aiki a hukumar NIA tun daga shekara ta 1995 kuma a shekarun da ya yi ya zauna a kasashen Koriya ta Arewa, Pakistan, Sudan, da kuma fadar shugaban kasa, inda ya kai ga mukamin darakata a hukumar ta NIA, kuma shi ne babban jami'in ofishin jakadancin Najeriya a Libiya. Shi kuwa sabon babban daraktan 'yansadan farin kaya na DSS wato Mr. Adeola Ajayi, ya yi ayyuka da dama kafin ya kai ga matsayin na yanzu wato mataimakin daraktan hukumar DSS, inda ya yi aiki a jihohin Bauchi, Enugu, Bayelsa, Rivers da jihar Kogi, inda daga nan ne ya samu wannan sabon mukami. Kakakin fadar shugaban Najeriya Chief Ajuri Ngelale ya ce shugaban kasar na fatan sabbin shugabannin na DSS da NIA za su yi aiki tare da ofishin mai baiwa shugaban kasa shawara kan tsaron don magance kalubalen da Najeriya ke fiskanta.