A jihar Jigawa da ke Najeriya har yanzu ana gudanar bukukuwar al'adar nan ta "Taushen Fage", wacce a ciki 'yan mata da samari kan yi tozali har ta kai su ga aure, duk da bayyanar wasu ababen zamani da ke gurbata al'adun da al'umma ke rike da su a wasu sassan Najeriya.