1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ukraine: Matsaloli saboda harin Rasha

March 7, 2023

Bayan kwashe shekara guda da mamayar Rasha a Ukraine, tattalin arzikin Kyiv din ya samu koma baya matuka sakamakon lalata cibiyoyin samar da makamashi da kuma hana hada-hada a tashoshin jiragen ruwan kasar saboda hari.

https://p.dw.com/p/4OK22
Ukraine | Yaki | Rasha
Masana'antu da gine-gine da dama sun lalace saboda yaki a UkraineHoto: Vojtech Darvik Maca/CTK/picture alliance

Sai dai duk da wannan Ukraine din na kokari wajen ganin wasu daga cikin kamfanonin kasar musamman ma na tama da karafa, sun ci gaba da aiki kamar yadda suke yi a baya. Yakin da ake yi a kasar ta Ukraine dai, ya yi sanadin dakatar da ayyukan kamfanoni da dama saboda yadda aka lalata wasu cibiyoyin samar da makamashi da suke amfani da su da ma toshe kafofin shigar da kayan da kamfanonin da suke amfani da su. Sai dai wani kamfani da ke sarrafa karfe a birnin Dnipro na ci gaba da gudanar da aikinsa, sai dai shugaban kamfanin ya ce suna aikin ne cikin yanayi na fargaba da kuma shirin ko-ta-kwana. Guda daga cikin irin shirin da masu kamfanoni a birnin na Dnipro suke yi shi ne, injinan samar hasken wutar lantarki sakamakon katsewar da ake ci gaba da samu daga lokaci zuwa lokaci musamman ma dai idan an kawo hari.

To sai dai duk da wannan ba kowanne kamfani ne zai iya jure amfani da injin samar da wutar lantarkin ba saboda tsadar da hakan ke da ita, amma kuma masu kamafanoni a wannan yanki sun ce suna ci gaba da zage damtse wajen ganin lamura sun ci gaba da tafiya daidai. Wadannan kamfanoni na Ukraine din dai na ganin ko ba komai za su samu kudin shiga wanda za su yi amfani da wani kaso daga ciki, domin biyan ma'aikatansu da nufin ganin sun biya bukatunsu na yau da kullum musamman ma dai sayen dan abin masarufi. A daura da wannan yunkuri da wasu kamfanonin ke yi na ganin sun tsaya kan kafafunsu duk da yakin da ake yi, wasu kuwa tuni sun rufe saboda yanyin da ake ciki. Wasu alkaluma da aka fitar a baya-bayan nan sun nuna cewar kimanin kaso daya bisa uku na kamfanonin kasar sun dakatar da aiki, lamarin da ya sanya tattalin arzikin Ukraine din ya shiga halin tasku..