1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

NATO na dari-darin mika wa Ukraine jiragen yaki

Mouhamadou Awal Balarabe
February 14, 2023

Ministocin tsaro na kasashe da ke da kujera a kungiyar tsaro ta NATO sun gudanar taro a birnin Brussels don neman hanyoyin gaggauta samar wa Ukraine da makamai da harsasai don kare kanta, amma ban da jiragen yaki.

https://p.dw.com/p/4NTsp
Sakataren tsaron Amirka Lloyd Austin da ministan tsaron Ukraine Oleksiy ReznikovHoto: Olivier Matthys/AFP

Sakataren tsaron Amirka Lloyd James Austin ya bayyana matsayar da kasashen NATO suka cimma, inda ya ce Amirka da Jamus da Holland suna aiki tare don samar wa Ukraine da makaman kare sararin samaniyarta. Su ma Faransa da Italiya sun hada gwiwa wajen samar da wasu karin fasahohin kare kai daga hare-hare makiya. Hakazalika wasu jerin kasashe da ke kawance da Ukraine ciki har da Poland da Kanada da Portugal da Spain sun yi shelar samar mata da tankokin yaki.

A nasa bangaren sakatare-janar na NATO Jens Stoltenberg ya yi gargadin cewa shugaban Rasha Vladimir Putin na shirin kai sabbin hare-hare a kasar Ukraine, don haka ya nuna mahimmancin kara tallafa wa Ukraine da makamai don ta kare kanta. Yawancin kasashen NATO na gaban kansu wajen ba wa Ukraine makaman da take bukata, amma kungiyar ta tsaro na ba da gudunmawa a wasu fannonin musamman ma shawarwari kan dabarun yaki. Duk da cewa babban sakatare NATO Jens Stoltenberg ya bayyana cewa kawayen Ukraine za su cika alkawarinsu na samar mata da makaman tinkarar Rasha, amma ya kawar da yiwuwar samar mata da jiragen yaki a yanzu.

Belgien | Treffen der Nato-Verteidigungsminister in Brüssel
Babban sakataren NATO Jens Stoltenberg a taron ministocin tsaro a BrusselsHoto: Johanna Geron/REUTERS

Jens Stoltenberg ya ce: "Batun jirage yaki ba shi ne mafi muhimmanci a yanzu ba, amma ana ci-gaba da tattaunawa akai kamar yadda na sha fada a baya. Sannan muna tuntubar juna tsakanin kasashen kawaye kan irin makamai ya kamata mu ba wa Ukraine. Irin tallafin da muke ba wa Ukraine ya canza kuma zai ci gaba domin ya dace da yanayin da wannan yaki ke gudana."

Ministan tsaron Ukraine Oleksiï Reznikov ya jadadda a cikin wani sako da ya wallafa  a shafinsa na twitter cewa kasarsa na bukatar isassun makamai don kare sararin samaniyarta. Dama dai Shugaba Volodymyr Zelensky wanda ya ziyarci London da Paris da Brussels a makon da ya gabata, ya yi kira da a samar wa Ukraine da jiragen yaki da makamai masu linzami masu cin dogon zango domin tinkarar sojojin Rasha. Amma ministan tsaron Jamus Boris Pistorius ya ce mambobin NATO na jan kafa wajen bai wa Ukraine jiragen yakin ne saboda da dalilai da dama.

Pitorius ya ce: "Ina ganin kowa ya fahimci cewa batun tsaron sararin samaniyar Ukraine da kuma batun sayan alburusai ya fi muhimmanci a halin yanzu fiye da tattaunawa kan jiragen yaki.Kowa ya san cewa horar da matukan jiragen yaki na daukar watanni da dama, baya ga koyar da su dabarun da ake bukata don amfani da makamai. Ya kamata mu mayar da hankali kan halin da ake ciki a fagen yaki, musamman harin da Rasha ke niyar kaiwa."

Belgien | Treffen der Nato-Verteidigungsminister in Brüssel
Ministan tsaron Jamus Boris Pistorius ya samu rufin bayan kwararru a kan tsaroHoto: Johanna Geron/REUTERS

Dakarun na Ukraine suna amfani da harsasai da ya zarta adadin da kasashe mambobin NATO ke kerewa, in ji sakatare janar na kungiyar tsaron Jens Stoltenberg. Amma ya ce a daidai lokacin da ake shirin cika shekara guda ta fara wannan yaki, Rasha ba ta da niyar ja da baya.

Sakataren NATO ya ce: " Ba mu ga alamun cewa Shugaba Putin na shirin samar da zaman lafiya ba, akasin haka ma dai muke gani. Yana shirin kara kai sabbin hare-hare, don haka yana da matukar muhimmanci NATO da kawayenta su ba da karin goyon baya ga Ukraine. Za mu hadu a karkashin kungiyar tuntubar juna kan Ukraine da Amirka ke jagoranta don samar da ingantaccen tallafi da samar da wadatatun harsasai da suka wajaba zuwa Ukraine." 

Deutschland Waffen für die Ukraine
Shigen tankokin yaki da Jamus ke shirin aika wa UkraineHoto: Martin Meissner/AP Photo/picture alliance

A karon farko kungiyar tsaro ta NATO ta yi amfani da taronta wajen bayyana yiwuwar shigar da Finland kafin Sweden cikin kawance. Amma sakatarenta Stoltenberg ya yi ikirarin cewa yana kokarin shawo kan Turkiyya da ta ki amincewa Sweden ta samu kujara a NATO.  A farkon watan Fabrairu ne shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya ce majalisar dokokin kasarsa za ta iya amincewa da shigar kasar Finland ba tare da amincewa da bukatar Sweden ba.