1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Duniya na iya fuskantar karancin man fetir

Abdourahamane Hassane AAI
September 16, 2019

Bayan da 'yan tawayen Houthis na Yemen masu samun goyon bayan Iran suka kai jerin hare-hare kan matatar man fetir din Saudiyya mafi girma farashin man fetir ya tashi a duniya.

https://p.dw.com/p/3Pg9C
Saudi-Arabien Raffinerie Ras Tanura
Hoto: Reuters/A. Jadallah

'Yan tawayen na Houthis na Yemen da ke samun goyoyn bayan Kasar Iran, sun kai hare-haren ne da jirage marasa matuka a kan matatar man fetir din Saudiyya mafi girma wacce ta kama da wuta a ransar asabar. Wanda a sanadin haka a yau an wayi gari farashin man fetir ya yi tasahin gwauron zabi a duniya. Wannan shi ne birkicewar lassafi mafi muni da aka taba samu a kan sha'anin kasuwar duniya ta man fetir, a sakamakon harin da jirage marasa matuka da 'yan tawayen Houthis na Yemen suka kai a kan matatar man Saudiya da ke  Abqaiq wacce ta kone, wanda hakan ya sa Saudiyya ta soke kusan rabin man fetir din da ta ke hakowa. Yanzu haka dai farashin gangar 'danyen man fetir din ya tashi da kishi 8 da rabi zuwa kishi 65 na dalar Amirka a London, yayin da a New York ya kai dala 59.