1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tarzoma ta tashi a Kano duk da dokar hana fita da aka kafa

August 3, 2024

Yayin da aka shiga rana ta uku ta zanga-zanga a Najeriya, hankali ya sake tashi a jihar Kano da ke arewacin kasar sakamakon sake fitowar masu bore da ya kaiga bude wuta.

https://p.dw.com/p/4j4yM
Wasu masu zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa a Najeriya
Hoto: Adekunle Ajayi/IMAGO/NurPhoto

A Najeriya an shiga kwana ta uku ta zanga-zangar kasa baki daya a kan tsadar rayuwa da rashin shugabanci na gari, inda ta rikide ta koma tarzoma a wasu sassana kasar a ranar farko.

A jihar Kano dai sabuwar tarzoma ta tashi a wasu yankunan jihar duk da dokar hana fita ta tsawon sa'o'i 24 da gwamnatin ta kafa, kamar yadda wakilinmu Nasir Salisu Zango ya ruwaito.

A jihar Filtao da ke tsakiyar kasar gwamnan jihar ne ya jinjina wa al'umar jihar saboda aiwatar da zanga-zangar lami lafiya duk kuwa da kaurin suna da Filaton ta yi wajen samun fitintinu a tsakanin mazaunanta.

Abuja fadar gwmantain kasar kuwa, dakon jawabi ake yi daga shugaban kasa Bola Tinubu a kan halin da ake ciki, kamar yadda wakilinmu Ubale Musa ya labarta.