1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tasirin Covid-19 kan tattalin arzikin kasashen Afirka

Mimi Mefo MAB/MNA
May 18, 2021

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya karbi bakoncin wasu shugabannin kasashen Afirka domin zakulo hanyoyin karfafa tattalin arzikinsu da annobar Covid-19 ta raunana.

https://p.dw.com/p/3tYjm
Frankreich l Macron wirbt für Sahel-Initiative
Hoto: Getty Images/AFP/G. Horcajuelo

Hanyoyin magance radadin annobar Coronavirus ne ajandar taron na kolin tsakanin Faransa da wasu shugabannin kasashen Afirka. Amma kuma sanin kowa ne cewa akwai abubuwa da ke hana ruwa guda a dangantakar Faransa da kasashen Afirka, kama daga ruwa da tsaki da take ci gaba da yi a kasashen da ta yi wa mulkin mallaka, i zuwa ga na taimako, da kuma amfani da kudin bai daya na Franc CFA. Tuni aka fuskanci takaddama game da ka'idojin da aka yi amfani da su wajen zaban mahalarta taron da Emmanuel Macron ya dauki bakoncinsa.

Roland Marchal, babban masani kan alakar Faransa da Afirka a Jami’ar Kimiyyar Siyasa da ke birnin Paris, ya ce ba a bayyana ka’idar da Macron ya bi wajen zaban mahalarta taron kolin ba.

Karin bayani: Faransawa ba sa son yaki a Mali

"Shugaba Emmanuel Macron ya aike da goron gayyata zuwa ga kasashen Afirka masu matukar karfin arziki da kuma wadanda ke cikin kungiyar La Francophonie. Ba daidai ba ne a dauka cewa manufar Faransa ita ce ta tattara kasashen da ta raina mambobin La Francophonie ba, wadanda sune abokan cinikinta na fil azam a nahiyar Afirka."

Amfani da takardun kudin CFA Franc a kasashen Afirka rainon Faransa na ci gaba da janyo cece kuce
Amfani da takardun kudin CFA Franc a kasashen Afirka rainon Faransa na ci gaba da janyo cece kuceHoto: picture-alliance/NurPhoto/A. Ronchini

Kamar dai magabatansa Francois Holland da Nicholas Sarkozy, Shugaba Emmanuel Macron ya yi kokarin fadada alakar kawance da kasashen da Faransa ba ta yi mulkin mallaka ba, kamar Habasha da Kenya da Najeriya da kuma Afirka ta Kudu. Dama masu lura da lamuran yau da kullum na kallon su a matsayin kasashen da suka fi samun bunkasar tattalin arziki na Afirka. Sai dai dan majalisar Faransa Sebastien Nadot ya bayyana dalilan da suka sa ba a gayyaci wasu shugabannin Afirka ba.

"Akwai batun tsoffin kasashen da Faransa ta raina. Tabbas kasashen da ke ci gaba da takaddama da Faransa ba za su halarci taron ba, idan ba haka ba, za a dauke shi a matsayin tsokana ga 'yan kasashen da ke da zama a Faransa. Misali, Sassou Nguesso na Kwango Brazzaville, ba shi cikin mahlarta taron na koli ba."

Karin bayani: Faransa tana katsalandan a siyasar Nijar

Babban burin da taron ya sa a gaba dai, shi ne ba da gudunmawa ga kasashen da Covid-19 ta jawo wa rauni a fannoni da dama. Saboda haka ne wasu 'yan Afirka ke fatan samun kyakkyawar makoma, kamar yadda Albert Rudatsimburwa, wani dan Ruwanda mai sharhi kan lamuran Afirka ke cewa.

"Tabbas, dama ce ga Afirka da annobar ba ta yi barna ba har ya zuwa yanzu, saboda haka a duk duniya, Afirka tana kan gaba. Amma zuwa taron da kungiyoyi masu yawa wadanda ke daukar nauyin allurar riga-kafin ta Covid-19 za su kasance wata dama ce ta tattaunawa kan yadda Afirka za ta ci gajiya."

Ba duka kasashen Afirka masu amfani da harshen Faransanci aka gayyata a taron kolin ba
Ba duka kasashen Afirka masu amfani da harshen Faransanci aka gayyata a taron kolin baHoto: picture-alliance/KEYSTONE/P. Klaunzer

Ga manazarciya 'yar kasar Kamaru Bergeline Ndoumou, akwai wasu batutuwan da suke ci wa nahiyar Afirka tuwo a kwarya, wadanda taron kolin Faransa ba zai tabo ba, musamman ma gudanar da shugabanci na gari tare da samar wa 'yan kasa ababen more rayuwa.

"A game da taron Faransa da Afirka, wannan wani kari ne na taruka marasa adadi da aka gudanar, bata lokaci ne. Ta yaya wadancan tarurrukan suka amfani Afirka? Shin muna da ruwan sha? Muna da makarantu masu kyau ko cibiyoyin kiwon lafiya? Ta yaya tarurrukan suka shafi salon shugabanci a kasashenmu na Afirka da dama? Har yanzu muna da shuwagabanni marasa kyau da mummunan salon tafiyar da mulki."

Karin bayani:Faransa za ta rage sojinta a yakin Sahel 

Ndoumou ta bayyana wannan taro a matsayin mara amfani, na bata lokaci da kayan aiki wanda ya fi amfani ga Faransa fiye ga nahiyar Afirka. Babu dai wata alama da ke nuna cewa taron zai tattauna wasu batutuwan da suka siyasa da zamantakewa, da kuma shugabanci na gari. Amma yawancin masu sharhi sun nuna cewa Faransa na nuna alamun damuwa game da halin da wasu kasashen Afirka ke ciki. Sai dai Mista Nadot ya zargi Faransa da neman wasa da hankalin 'yan Afirka, inda take neman warware matsalolin kudi na Afirka yayin da ta kasa magance nata.