1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Faransa za ta rage sojinta a yakin Sahel

Binta Aliyu Zurmi
January 8, 2021

Shugaba Emmanuel Macron na Faransa  ya ce za akwai bukatar sauya salon yadda akeyakar 'yan ta'adda a yankin Sahel da kuma yiwuwar rage wasunsu.

https://p.dw.com/p/3nfQD
EU-Gipfel in Brüssel | Emmanuel Macron, französischer Präsident
Hoto: Olivier Hoslet/REUTERS

Shugaba Macron ya bayyana hakan ne a yayin da yake ta'aziyyar mutuwar wasu dakarun sojin kasar a wani hari da aka kai musu a kasar Mali. An gudanar da taro a birnin Paris domin tunawa da sojojin biyu da suka rasa rayukansu a fagen yaki da 'yan ta'adda. Ana sa ran zai yi cikkaken bayani a wani taron koli da ya kunshi babban shirin rundunar sojin Faransa a birnin Ndjamena na kasar Chadi a watan gobe.

Ministan tsaron Faransa Jean Yves Le Drian  ya ce akalla dakarunsu dubu biyar ne za su janye daga yanklin na Sahel. Tun a shekarar 2013 ne sojin Faransa suke a kasar Mali kafin daga bisani a wani mataki na tabbatar da karin tsaro a yankin suka bazu har ya zuwa kasashen Chadi da Nijar da Burkina Faso da kuma Moritaniya.