1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar ba za ta taron Faransa da Afirka ba

Gazali Abdou Tasawa LMJ
September 29, 2021

Faransa ta aike wa da wasu kungiyoyin farar hula na Jamhuriyar Nijar da goron gayyata, zuwa taron koli na Faransa da Afirka da zai gudana a birnin Montpellier na Faransar daga ranar bakwai zuwa tara ga watan gobe.

https://p.dw.com/p/412lZ
Internationale Libanon Konferenz | Präsident Macron Frankreich
Shugaban kasar Faransa Emmanuel MacronHoto: Christophe Simon/AFP/AP/picture alliance

To sai dai kawancen kungiyoyin farar hula na Nijar, ya yi watsi da goron gayyatar zuwa wannan taro da a karon Farko Faransar za ta shirya tare da kungiyoyin farar hula na Afirka sabanin shugabannin kasashen nahiyar da ta saba yin taron da su. A cikin wata wasika da ta aike Nijar din, kasar ta Faransar ta gayyaci kawancen kungiyoyin farar hula na Tournons La Page reshen Nijar domin halartar wannan taron koli na Faransa da Afrika.

Karin Bayani: Taron kolin Faransa da Afirka kan Covid-19

To sai dai kungiyar ta Tournons La Page  a Nijar din, ta ce ita kam ba za ta halarci wannan taro ba. Sai dai kuma kungiyar farar hula ta DHD ta bakin shugabanta Kabirou Issa wacce ba a gayyata a wannan taro ba, na ganin babban kuskure ne ga kungiyar ta Tournons La Page ta kauracewa wannan taro na birnin Monpellier. A shekara ta 1973 ne Faransa ta assasa wannan taron koli da aka fi sani da Sommet Afrique-France, inda take gayyatar shugabannin kasashen Afirka.

Frankreich-Afrika-Gipfel
Hoto: Reuters/L. Gnago

Amma a karon farko a wannan shekarar Faransa ta sake tsari, inda ta gayyaci kungiyoyin farar hula na Afirkan a madadin shugabanni. Kungiyoyin fafutukar na kasashen Afirka da suka dauki matakin bijire wa taron na birnin Montpellier dai, sun sanar da shirin tsara wani taron kishiyar na mahukuntan kasar ta Faransa a birnin na Montpellier.

Karin Bayani: Taron Afirka da Faransa karo na 27 a Mali

Za dai su gudanar da taron a lokaci guda da wanda Faransan ta shirya, inda za su fallasa abin da suka kira zalincin da Faransan ke yi wa kasashen Afirka shekaru da dama da kuma fito da shawarwari na kalubalantar manufofinta a Afirka wanda Faransar ta assasa tun a shekara ta 1973, da kuma take shiryawa bayan kowadanne shekaru biyu a  ke shiryawa a kowadanne shekaru biyua wannan taro na birnin Montpellier wanda a karon farko Faransar tu bayan da Farans ata assasashi a shekara ta 1973