1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron duniya kan halin da 'yan gudun hijira ke ciki

Karin Bensch ZMA/MNA
December 18, 2019

A daidai lokacin da matsalar 'yan gudun hijira ke kara kamari a duniya, an bude wani taron yini uku, irinsa na farko don duba halin da 'yan gudun hijira ke ciki dama irin tallafi da za a ba su.

https://p.dw.com/p/3Uxou
Schweiz Genf Global Refugee Summit
Antonio Guterres da Ignazio Cassis, ministan harkokin wajen Switzaland da Filippo GrandiHoto: AFP/S. Di Nolfi

Taron da ke gudana a birnin Geneva na kasar Switzaland na da nufin musayar bayanai tsakanin kasashen da ke tsugunar da 'yan gudun hijiran da suka fito daga kasashe dabam-dabam da a yanzu yawansu ya zarta miliyan 20.

Wannan taro na zuwa ne shekara guda bayan da zauren mashawartar Majalisar Dinkin Duniya ya amince da wani shiri da ke da burin samar da hanyoyin da za a bi na taimaka wa 'yan gudun hijira da ma al'ummomin da suka ba su matsugunni.

Shugabannin gwamnatoci da kasashe da manyan 'yan kasuwa da kwararru a fannin ba da agaji za su yi musayar bayanai da ma yadda za su agazawa wannan rukuni na mutane. Filippo Grandi shi ne kwamishinan kula da 'yan gudun hijira na Majalisar Dinkin Duniya.

"Kasashen Costa Rica da Turkiyya da Ethiopiya da Jamus wadanda suka yi hadin gwiwar daukar nauyin taron da hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya, sun kasance a sawun gaba-gaba wajen fuskantar matsalolin kwararar 'yan gudun hijira a 'yan shekarun da suka gabata. Kuma sun taimaka wajen wayar da kai dangane da tallafa wa manufofin ceton 'yan gudun hijurar."

Kelly T. Clements, mataimakiyar babban kwamishinan kula da 'yan gudun hijira
Kelly T. Clements, mataimakiyar babban kwamishinan kula da 'yan gudun hijiraHoto: picture-alliance/AP Photo/Keystone/M. Trezzini

A cewar hukumar kula da 'yan gudun hijirar dai yaki da rigingimu sun kori mutane sama da miliyan 70 daga matsugunnansu. Kusan miliyan 26 daga cikinsu 'yan gudun hijira ne, rabinsu kananan yara masu shekaru kasa da 18, wadanda suka tsallake kan iyakokin kasashe dabam-dabam kuma suka gaza komawa yankunansu na asali.

Sai dai a cewar daraktar kula da da bangaren dangantakar ketare ta hukumar 'yan gudun hijirar Dominique Hyde, taron zai aike da sakon da ke nunar da cewar, kowane mataki na da muhimmanci, kamar yadda kowane mutun yake da daraja.

A cewar hukumar, shawo kan matsalolin 'yan gudun hijirar na bukatar goyon baya daga dukkan bangarori na al'umma, kuma akwai kamfanoni sama da 100 da ke cikin wannan taro. Dominique Hyde ta kara da cewar tilas ce ke sa mutum ya guje wa matsuguninshi na asali.

'Yan gudun hijirar Sudan ta Kudu a sansanin 'yan gudun hijira na Kakuma da ke a kasar Kenya
'Yan gudun hijirar Sudan ta Kudu a sansanin 'yan gudun hijira na Kakuma da ke a kasar KenyaHoto: Getty Images/AFP/T. Karumba

"Mutane na gudu saboda dalilai dabam-dabam, wasu na gudu saboda rikici, wasu kuma saboda yaki, mutane kazalika na gudu saboda matsalolin yanayi. Amma abin da ke da muhimmanci shi ne babu wanda ke son guduwa ya bar asalinsa, kowa ya gwammace zama a gidanshi, ya ci gaba da tafiyar da ayyukanshi tare da rayuwa cikin iyalinsa."

A cewar wani likita da ya dauki tsawon shekaru yana aikin agaji a sansanin 'yan gudun hijira na Kakuma da ke yankin Arewa maso Yammacin kasar Kenya, da ke dauke da 'yan gudun hijira daga kasashe makwabta musamman Sudan ta Kudu, ilimi na daga cikin abin da wannan rukuni na mutane ke bukata musamman yara kanana. A kan haka ne ma ya kaddamar da wani shiri na bai wa  yaran darasi.

"Wannan wani shiri ne na karantar da yara da maraice. Suna wasanni da addu'o'i. Kazalika suna koyon harsunan Ingilishi da Kisuwahili. Hakan na taimaka musu wajen ingantuwar iliminsu da fahimta don rayuwarsu a nan gaba."