Kamar yadda masu sauraro suka tambaya a cikin filinmu na Amsoshin Takardunku, DW Hausa ta tattauna da Dakta Umma Aliyu Malama a sashin nazarin harsunan Afirka na Jami'ar Hamburg da ke nan Jamus, wadda ta bamu takaitaccen tarihin fitaccen malamin mai kula da nazarin harshen Hausa a Jami'ar Bayero da ke Kano Dakta Habibu Sani Babura da Allah ya yi wa rasuwa a makon da ya gabata.