1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Chaina ta yi barazana wa 'yan Taiwan saboda zabe

Abdourahamane Hassane
January 13, 2024

Al ummar Taiwan na kada kuri'a a zaben shugaban kasa da na 'yanm majalisun dokoki karkashin barazana daga Chaina wacce ke ikirarin mallakar tsibirin kuma ta yi kira garesu da su yi zabin da ya dace.

https://p.dw.com/p/4bCDL
Taiwan Wahlkampf 2024 | Democratic Progressive Party | Anhänger
Hoto: Carlos Garcia Rawlins/REUTERS

'Yan takara guda uku ne dai ke fafatawa a zaben a ciki har da shugaban mai barin gado Tsai Ing-wen. Mataimakin shugaban kasar Lai Ching-te na jam'iyyar DPP, wanda ake hasashen zai samu nasara, Chaina na yi masa kallon babban hadarin saboda manufofinsa na samun yanci Taiwan din. Yanki mai yawan al'umma miliyan 23da ke da tazarar kilomita 180 daga gabar tekun kasar China, ana  yaba masa a matsayin abin koyi na dimokuradiyya a  nahiyar Asiya: Zaben da zai kammala tun zagayen farko, tuni da aka bude runfuna zabe da karfe takwas agogon GMT kuma za a rufesu da misalin karfe hudu ,tare da sa ran samun  sakamakon zaben  da yaTaiwan da Chaina rikici na ta'azzaramma.