1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikici na kara ta'azzara tsakanin Chaina da Taiwan

Abdoulaye Mamane Amadou SB
April 9, 2023

Manyan kasashen duniya na jan hankalin Chaina game da atisayen sojan da take na sama da na ruwa a tekun Taiwan, wanda ta kira na tauna tsakuwa don aya ta ji tsoro.

https://p.dw.com/p/4PqwI
China startet dreitägige Militärübungen rund um Taiwan
Hoto: picture alliance/dpa/CCTV/AP

Chaina ta ce ta gwada kaddamar da wasu jerin hare-hare a muhimman abube na tekun Taiwan, a ci gaba da atisayen sojin da take a rana ta biyu kusa da tsibirin, duk da kakkausar sukar da ta ke sha daga wasu manyan kasashen yamma ciki har da Amirka.

Sabon atisayen mai suna "Joint Sword" na a matsayin tauna tsakuwa don aya ta ji tsoro ne da Bejin ke yi, a wani mataki na mayar da martani kan ziyarar shugabar yankin Taiwan a Amirka.

Tuni ma dai ma'aikatar tsaron Taiwan ta tabbatar da ganin dandazon jiragen ruwa na yakin Chaina 9 da 58, kana Taipei ta ce ta fargar da dakarunta da su kasance cikin shirin ko ta kwana.