1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taba Ka Lashe: 19.06.2024

June 25, 2024

Shiri ya duba sana'ar farauta sana'a wacce ta samo asali tun wanzuwar 'dan Adam a doron kasa, kamar yadda tarihi ya nuna, inda dukkan kabilun duniya ke da nasu nau'in na salon yadda suke gudanar da farautar.

https://p.dw.com/p/4hThQ
Hoto: Lino Mirgeler/dpa/picture alliance

Farauta dai mashahuriyar sana'a ce a duniya, wadda ke zama hanyar neman abinci da kayayyakin ado da fatun namun dajin da aka kaso, baya ga amfani da naman a matsayin abinci. A gefe guda kuma a kan yi amfani da wani bangare na namun dajin domin hada laƙani da kuma magunguna iri-iri. A kasar Hausa dai farauta na cikin jerin sana'o'in da suka yi fice a gargajiyance. Daga za a iya sauraran sauti