1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya tana fama da matsalolin tsaro

May 28, 2024

Bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kwashe shekara guda bisa mulkin Najeriya, na kallon ta‘azzarar rashin tsaro duk da karuwar kudaden yakar annobar a karkashin ta gwamnatin kasar.

https://p.dw.com/p/4gOAr
Taron Majalisar Tsaron Najeriya karkashin Shugaba Bola Ahmed Tinubu
Taron Majalisar Tsaron Najeriya karkashin Shugaba Bola Ahmed TinubuHoto: Ubale Musa/DW

Kudin kasar kimanin Naira triliyan kusan biyu, ko kuma kaso bakwai cikin dari na daukacin kasafin Najeriya na shekarar bana ne dai sabin mahukuntan suka ware domin yakar rashin tsaron. To sai dai kuma shekara guda bisa mulki, batun rashin tsaron na dada kamari walau cikin tsakiyar Najeriya, ko kuma sashen arewa maso yammacin kasar da ke zaman tunga ta barayin daji.

Karin Bayani: Afrika na laluben mafita daga ta'addanci

Jami'an tsaron Najeriya
Jami'an tsaron NajeriyaHoto: Afolabi Sotunde/REUTERS

Wata sabuwar kiddidiga ta kamfanin Beacon Consult da ke nazarin rashin tsaro cikin kasar dai ta ce, Najeriya ta kalli karuwar rashin tsaro a karkashi ta gwamnatin ta Bola Tinubu. Kuma Kabiru Adamu dai na zaman shugaba na Kamfanin da ya ce kiddidgar ta nuna karuwa daga shekarar karshe ta tsohuwar gwamnatin Muhammdu Buhari, ya zuwa shekarar farko a gwamnatin Tinubu cikin batun rashin tsaron mai tasiri.

Ya zuwa yanzu dai masu mulki na Abuja na ikirarin takama da makamai na zamani domin tunkarar rikicin rashin tsaron dake sauyin launi. Dubban miliyoyin na daloli ne dai Abuja ta kai ga kashewa a kokari samar da tsaron da ya mayar da jami‘an tsaron kasar na kan gaba a yankin ECOWAS. To sai dai kuma shekara guda ta mulkin Tinubu dai a tunanin Murtala Aliyu da ke zaman sakatare na kungiyar dattawan arewacin kasar ACF ana bukatar sake tashi tsaye da nufin ceto kasar cikin batun rashin tsaron da ke iya tasiri har ga rayuwa da makoma. Tuni dai dama batun rashin tsaron ke tasiri ga kokarin kasar da ke ta karuwar hauhawar farashin abinci.