1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

HdM: Matashi mai gyaran wayar salula

May 18, 2022

Wani matashi a Jihar Sokoton Najeriya da ya kammala digiri ya rungumi sana'ar gyaran wayar salula a zamanance.

https://p.dw.com/p/4BT9m
Fraunhofer IZM | Untersuchungen zur Reparierbarkeit von Smartphones
Hoto: Fraunhofer IZM

Shi dai matashin Yahaya dogon Daji ya na horar da rukuni-rukuni ne na matasa yadda za su iya gyara wayar salula ne. Kungiyoyi da gwamnatoci na kawo darurruwan matasa har da mutane masu bukata ta musamman a hannun wannan matashi don a koyar da su sana'o'in hannu na gyaran wayar salula. Matashin dai ya kware a wannan fanni duk ko da yake ba abun da ya karanta ba a jami'a. Matashin ya ce a cikin sana'ar yake ci ya sha har ya gudanar da harkokin rayuwarsa ta yau da kullum. Yanzu haka dai Yahaya Dogon Daji kungiyoyi da gwamantoci na daukarsa horar da matasa dubarun gyaran waya don suma su zamo masu dogaro da kai.