1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sojoji a Gabon na gudun maimaita kura-kuran baya

Binta Aliyu Zurmi
September 2, 2023

Sojojin da suka kifar da gwamnatin Shugaba Ali Bango sun bayyana cewar ba za su yi hanzarin mayar da kasar rumfunan zabe ba, don gudun kaucewa kura-kuran da aka tafka a baya.

https://p.dw.com/p/4VsKy
Gabun | General Brice Oligui Nguema
Hoto: AFP/Getty Images

A wata sanarwa da Janar Brice Oligui Nguema ya yi a gidan talabijin din kasar da yammacin jiya Juma'a, ya tabbatar da cewar za su yi sauri wajen mayar da kasar tafarkin dimukradiyya, amma bisa ka'idojin kasa da kasa da suka bada damar mutumta farar hula da samar da kyakyawan mulkin al'umma. A yayin da suke ci gaba da shan matsin lamba na mayar da kasar ga mulkin farar hula.

Hakan na zuwa ne yayin da jam'iyyun adawan kasar ke neman sojojin su amince da nasarar da dan takararsu ya samu a zaben  da aka gudanar.

 

Karin bayani: 'Yan adawa a Gabon na neman a ba su mulki

A ranar Larabar da ta gabata ce sojojin Gabon suka kifar da gwamnatin Ali Bango wanda ya kawo karshen mulkin sama da shekaru 50 da suka yi shi da mahaifinsa, Juyin mulkin da ya kasance na takwas a Yammaci da Tsakiyar Afirka cikin shekaru uku.

Tuni sabuwar gwamnati rikon kwarya da ake shirin rantsar da shugabanta ta fara canje-canje a kasar ciki harda mayar da ranar 30 ga watan Augusta ranar da aka kwace mulki daga Bango ya zuwa ranar yancin kasa.