1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Muna shirye don tattaunawa da kungiyar ECOWAS -Sojojin Nijar

Abdoulaye Mamane Amadou Abdul-Raheem Hassan
August 13, 2023

Sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar sun bayyana cewa a shirye suke da su hau kan duk wani teburin tattaunawa da ECOWAS domin warware dambarwar siyasar kasar

https://p.dw.com/p/4V7QK
Chef der nigerianischen Präsidentengarde Tchiani erklärt sich nach dem Putsch zum neuen Anführer
Jagoran juyin mulkin Nijar Janar Abdourahmane Tchiani da mukarabansaHoto: Balima Boureima/picture alliance/AA

Majalisar sojojin da suka yi juyin mulki a Jamhuriyar Nijar sun bayyana shirinsu na hawa kan duk teburin tattaunawa da ECOWAS domin warware dambarwar siyasar kasar da ta barke tun bayan karbe mulki da tsinin bundiga a ranar 26 ga watan Agusta.

Sojojin sun bayyan haka ne a yayin ganawar da suak yi da wata tawagar jagororin addinai daga makwabciyar kasar Najeriya a birnin Niamey, wanda suka ce sun yi hakan ne da zummar buda wata kafa ta samun sauki ga kallon mai bisa ruuwa da bangaren sojan ke yi wa juna da kungiyar ECOWAS bayan hambarar da gwamnatin Mohamed Bazoum.

Wannan na zuwa ne a yayin da taron 'yan majalisun dokokin kungiyar ECOWAS ya yi fatali da gagarumin rinjaye da amfani da karfin bindiga wajen mayar da dimukradiyya a Nijar a yayin wani taronsu na ranar Asabar, inda suka bukaci kungiyar ta aika wata tawagar da za ta gana da sojojin.