1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Siyasar karba-karba a shugabancin Najeriya

Uwais Abubakar Idris
January 14, 2022

A Najeriya batun karba-karba a tsakanin yankunan kasar na cigaba da daukar hankali a dai- dai lokacin da mutanen da ke neman takarar shugabancin Najeriyar ke fitowa a manyan jamiyyu biyu na kasar

https://p.dw.com/p/45Y6s
Shugaban Najeriya Muhammadu Burai da Bola Ahmed Tinubu ke tattauna zaben 2023
Shugaban Najeriya Muhammadu Burai da Bola Ahmed Tinubu ke tattauna zaben 2023Hoto: Official-State House Abuja Nigeria

Ci gaba da samun mutanen da ke fitowa don nuna sha’awarsu ta neman takarar shugaban kasa a Najeriyar ya sake farfado da fagen siyasar kasar da tuni aka fara shirin babban zaben 2023. Kasa da mako guda bayan da jamiyyar APC ta karbi bukatun masu sha’awar takara, ita ma jamiyyar PDP ta bi sahu inda fitaccen dan jaridar nan Dele Momodu ya bayyana sha’awar takarar shugabancin kasar 

‘’Yace lokaci ya yi da za’a samu sasantawa da yafe wa juna da kuma rufe abubuwan da suka gabata, Najeriya na bukatar a sake yi mata saiti a kan inda ta dosa, shi yasa bayan tuntubar iyalaina da abokan arziki na yanke shawarar shiga takararar neman shugabancin Najeriya a jamiyyar PDP’’.

To sai dai a yayinda ake ci gaba da samun mutanen da ke nuna sha’awar zama shugaban Najeriya duk da cewa ana sauran fiye da shekara guda a yi zabe, batun karba karba na zama abinda ke haifar da rudani. Daga jamiyyar APC mai mulki zuwa ta PDP ta ‘yan adawa duka batun daya ne na karba-karba da ya sanya jamiyyun a tsaka mai wuya. Dr Ibrahim Bello Dauda jigo ne a jamiyyar APC mai mulkin Najeriyar da shi ma ya nuna sha’awarsa ta shugabancin kasar.

Duk da cewa duka manyan jamiyyun biyu na APC mai mulki da PDP ta ‘yan adawa sun bari batun karba-karaba na yawa a tsakanin ‘yayansu, inda ‘yan siyasa daga yankin kudu maso gabashin Najeriyar ta kaisu ga bayyana dole a barsu su dana shugabancin Najeriyar, amma alamu na nuna tafiya ta nuna kokarin gwada dabara inda kowace jamiyya ke kama hanyar barin kofa a bude kowa ya gwada sa'a. 

Da alamu fagen siyasar Najeriyar na kara zabura da batun takarar shugaban kasa a 2023  a yanayi na hangen dala ba shiga birni ba, abinda tuni ya fara shafar yadda ake gudanar da gwamnati a yanzu inda harkar siyasar ta fara daukar hankali da kawo cikas ga duk wani aiki na kasa.