1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cibiyar SIPRI na fargabar shiga rudani

Ralf Bosen ZMA/LMJ
May 23, 2022

Cibiyar binciken zaman lafiya ta kasa da kasa SIPRI, na ganin cewar duniya tana fuskantar barazanar tsaro mai sarkakiya da rashin tabbas.

https://p.dw.com/p/4Bjkb
Dan Smith I SIPRI
Babban daraktan cibiyar SIPRI Dan Smithz Hoto: Karin Tornblom/TT/picture alliance

A cewar cibiyar ta SIPRI dai, ga dukkan alamu gwamnatoci da mahukunta ba sa shirin da ya kamata don tunkarar wannan sabon yanayi. Cibiyar mai matsuguni a kasar Sweden da kuma ke nazarin zaman lafiya da tsaro dai, kan gabatar da rahotonta a kowace shekara dangane kudin da kasashe ke kashewa wajen sayen makamai. A wannan karon cibiyar ta yi nuni da irin hadari da barazanar da duniya ke ciki ba tare da wani tanadi ba, inda ta yi magana kan yanazin zamantakewa na lafiya da kuma tsaro. Cikin rahoton nata dai, SIPRI ta nunar da cewa duniya na cikin wani wadi na tsaka mai wuya na gurbacewar muhalli da karuwar barazanar rashin tsaro.

Karin Bayani: An kashe Euro sama da tiriliyan daya kan sojoji

Kama daga lalata dazuka da narkewar dusar kankara da robobin da ake jefawa cikin teku, wanda ta ce na da alaka da karuwar mace-mace ta hanyar rikice-rikice da dillancin makamai da ma kuma karuwar yunwa. Cututtuka kamar wadanda coronavirus ta janyo dai, sun haifar da karin hadari. A hirarsa da tashar DW babban daraktan cibiyar da ke Stockholm Dan Smithz ya nunar da cewa, barazanar rashin tsaro da lalacewar muhalli manyan matsaloli ne guda biyu da ke da alaka da kuma tasiri a kan juna. Rahoton na SPRI dai da ke zuwa gabanin taron zaman lafiya da ci-gaba karo na tara a birnin na Stockholm, tamkar tunatarwa ce ga 'yan siyasa da sauran masu ruwa da tsaki na lamuran duniya.

USA | Amirka | M777
Fargabar fadarwa duniya cikin sarkakiyar rashin tsaro da rikice-rikiceHoto: U.S. Marines/ZUMAPRESS/picture alliance

Daraktan cibiyar ya ce wasu gwamnatoci na sane da tsananin illar lamarin, amma  hankalinsu na kan wasu abubuwa na dabam. Mawallafa rahoton 30 daga Cibiyar Nazarin Zaman Lafiyar da wasu cibiyoyi, sun cimma matsaya cewa: "Akwai yiwuwar duniyar dan Adam ta samu wadata fiye da yadda ta kasance a baya, amma kuma akwai karuwar matsalar rashin tsaro." A cikin rahoton mai shafuka 93, sun bayyana sakamakon da al'amuran yaki ke iya haifarwa a duniya, ganin yadda duniyar ta kasance dukulalliya. Sauyin yanayi da ke haifar da bala'o'in yanayi da cutar Corona, na barazana ga hanyoyin samar da kayayyaki a duniya.

Karin Bayani: Amirka ce kan gaba wajen sayar da makamai

Tashe-tashen hankula da rashin samun amfanin gona, na daga cikin matsalolin da suka jefa manoma cikin halin ni 'yasu da karuwar kaura a duniya. Kuma kasashen da suka fi fuskantar wannan matsala, kasashe ne da ke fama da talauci da rashin shugabanci na gari. Rahoton ya bayar da misali da Somaliya da ta jima cikin matsalar fari da talauci, inda rashin gwamnati mai karfi ya tilasta mutane fadawa hannun tsagerun kungiyar al-Shabaab. Kazalika Afirka ta Tsakiya, na cikin yankunan da ke fama da matsanancin talauci.