1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAsiya

SIPRI: Duniya ta kashe kusan Euro tiriliyan biyu kan sojoji

April 25, 2022

Manyan kasashen duniya biyar da suka fi kashe kudaden kan sojoji da makaman yaki sun hada da; Amirka da China da Indiya da Birtaniya da kuma Rasha. 

https://p.dw.com/p/4APLK
Russland Sarmat-Interkontinentalrakete
Hoto: RU-RTR Russian Television/AP/dpa/picture alliance

Kudaden da duniya ke kashewa kan sojoji da samar da makamai sun kusan Euro tiriliyan biyu a karon farko a tarihin duniya. Cibiyar bincike kan zaman lafiya ta duniya, SIPRI, a cikin rahoton da ta fitar a wannan Litinin ta ce an kashe wadannan kudade ne a shekarar da ta gabata kadai. Kudaden sun haura abin da duniya ta kashe a shekara ta 2012 a kan  harkokin soji da sama da kaso 12 cikin 100.

Wani babban jami'i a cibiyar ta SIPRI Diego Lopes da Silva ya ce duk da yadda tattalin arzikin duniya ya samu tawaya sakamakon zuwan corona, kasashe dabam-dabam sun kara azama wurin kimtsa rundunoninsu na soji.