1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAmurka

Trump ya tsallaka rijiya da baya a harin bindiga

July 14, 2024

Hukumar tsaro ta Amurka FBI ta tabbatar da cewa an yi yunkurin halaka tsohon Shugaban kasar Donald Trump bayan da wani dan bindiga dadi ya bude masa wuta a lokacin yakin neman zabe a jihar Pennsylvania.

https://p.dw.com/p/4iGGA
An harbi Trump a gurin yakin neman zabe
An harbi Trump a gurin yakin neman zabeHoto: Brendan McDermid/REUTERS

Wani dan bindiga ya harbi tsohon Shugaban Amurka Donald Trumpyayin da yake jawabi a wani gangamin yakin neman zabe a jihar Pennsyvania.

Hutunan da aka wallafa a kafafen sadarwa sun nuna yadda tsohon shugaban kuma dan takara a zaben watan Nowamba ya ji rauni a kunnensa inda masu kare lafiyasa suka fitar da shi daga gurin taron jini na zuba daga fuskarsa. 

Rahotannin sun ce jami'an tsaro sun harbe maharin, sai dai ba a gano dalilansa na yunkurin halaka Trump ba.

A cikin wata sanarwa hukumomin tsaron Amurka sun tabbatar da cewa Trump na cikin koshin lafiya kuma ana ba shi cikakkiyar kariya, sannan kuma an fara bincike kan lamarin.

Jim kadan bayan harin Shugaban Joe Biden ya yi tir da Allah wadai da lamarin, 'yan siyasa daga bangarori dabam-dabam na aike wa da sokon jajantawa ga dan takaran na jam'iyyar Republicain mai shekaru 78 a duniya tare da nuna alhini kan abinda suka kwatanta da cin fuska ga tsarin dimukuradiyyar duniya.

Sai dai da alama babu sakon alhini daga gwamnatin Rasha kamar yadda kakain fadar Kremlin ya nunar. "Ba mu gaskata cewa gwamnati ce ta tsara ƙoƙarin kashe Trump ba." A cewar Dmitry Peskov.

A baya bayan nan kasar Amirka ta fuskanci kazamin hare-haren 'yan bindiga wanda ya kai ga bukatar tsaurara matakan takaita mallakar lasisin bindiga a hannun jama'a.