Shugabannin Afirka za su tattauna batun Boko Haram
April 8, 2015Talla
Taron wanda aka shirya zai samu halartar shugabannin daga ƙasashen Nijar da Kamaru a Chadi da Najeriya, na da manufar ƙaddamar da wani tsarin na bai ɗaya na haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen.
Domin yaƙi da Ƙungiyar Boko Haram wacce ke kai hare-hare na ta'addanci a cikin ƙasashen Najeriyar da Nijar da Kamaru da kuma Chadi. A wani rahoton da ta bayyana Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce tashin hankali na Boko Haram a cikin shekaru shida ya yi sanadiyyar mutuwar mutane dubu 15 a Najeriyar.