1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaLatin Amurka

Chile ta yi watsi da sakamakon zaben Venezuela

Suleiman Babayo ATB
August 7, 2024

Shugaba Gabriel Boric na kasar Chile ya yi watsi da sakamakon zaben Venezuela tare da kiran ganin an tantance kuri'un da aka kada, domin kawo karshen sabanin da aka samu tsakanin gwamnati da 'yan adawa na Venezuela.

https://p.dw.com/p/4jDXN
Shugaba Gabriel Boric
Shugaba Gabriel Boric na kasar ChileHoto: Kay Nietfeld/dpa/picture alliance

Shugaba Gabriel Boric na kasar Chile ya bayyana cewa kasarsa ba ta amince da Shugaba Nicolas Maduro na Venezuela a matsayin wanda ya lashe zaben kasar da aka gudanar a karshen watan jiya na Yuli ba. Haka ya nuna shugaban na Chile mai ra'ayin gaba-dai gaba-dai ya bi sahun kasashen Guatemala, da Ajentina da Peru gami da wasu kasashen na Latin Amirka bisa watsi da sakamakon zaben na Venezuela yayin da kasashen Brazil and Mexiko da ke da tasiri a yankin suka dauki matakin shiga tsakanin domin magance rikicin siyasar kasar ta Venezuela.

Karin Bayani: Shakku kan sahihancin sakamakon zaben Venezuela

Shugaba Boric na Chile ya bukaci ganin kungiyoyin kasashen duniya sun tantance kuri'un da aka kada, sai dai bai fito fili ya goyi bayan Edmundo Gonzalez wanda ke zama dan takarar bangaren adawa a zaben na kasar ta Venezuela.

A wani labarin jagoran 'yan adawan na Venezuela, Edmundo Gonzalez ya yi watsi da amsa gayyar da kotun kolin kasar ta yi masa a wannan Laraba kan zargin aikata manyan laifuka da babban mai gabatar da kara na kasar ya shigar, abin da ka iya zama saba umurnin kotu.