1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kais Saied ya lashe zaben raba gardama

Lateefa Mustapha Ja'afar RGB
July 26, 2022

Al'ummar Tunusiya sun amince da sabon kundin tsarin mulki da ya kara wa Shugaba Kais Saied karfin iko. An cimma matakin bayan kada kuri’ar raba-gardama.

https://p.dw.com/p/4EgIJ
Tunesien Präsident Kais Saied
Hoto: Zoubeir Souissi/REUTERS

Wani rahoto da kamfanin bincike da tattara bayanai na Sigma Conaeil ya fitar, ya nunar da cewa kaso 92 cikin 100 na kuri'un da aka kada sun nuna amincewa da sabon kundin tsarin mulkin. Bayan kwashe tsawon lokaci ana tayar da jijiyoyin wuya sakamakon karfa-karfar da ake ganin Shugaba Kais Saied na Tunusiyan na kokarin yi bayan da ya rushe gwamnati tare da dakatar da majalisar dokoki, a karshe al'ummar kasar sun kada kuri'ar raba-gardama domin kawo gyararraki a kundin tsarin mulki.

Tunesien Anhänger von Präsident Kais Saied feiern neue Verfassung
Yan kasa masu goyon bayan Shugaba Kais SaiedHoto: ZOUBEIR SOUISSI/REUTERS

Sai dai Hukumar zaben kasar ta bayyana cewa, bayan da 'yan adawa suka kauracewa zaben, kaso 27 da digo biyar na al'ummar kasar da suka cancanci kada kuri'a ne kacal suka fito domin kada kuri'unsu a zaben raba-gardamar. Sabon kundin tsarin mulkin zai bai wa Shugaba Kais Saied damar korar jami’an gwamnati daga aiki da nada alkalai da kuma bai wa sojoji umurni.

Tsohon kundin tsarin mulkin da aka amince da shi a shekara ta 2014, ya bai wa firaminista karfin iko fiye da shugaban kasa. Masu adawa da tsarin, na zargin Shugaba Saied da jefa Tunusiya cikin yanayi na mulkin kama-karya. A shekara ta 2011, Tunusiya ta kasance cikin kasashen da suka cimma nasara yayin kadawar guguwar juyin-juya halin kasashen Larabawa da ta yi gaba da kujerar mulkin tsohon shugaban kasar marigayi Zine el-Abidine Ben Ali.