1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaba kais Saied na fuskantar barazana

Mouhamadou Awal Balarabe
June 24, 2022

Ma'aikatar cikin gida ta Tunisiya ta nunar da cewa shugaban kasa Kais Saied na fuskantar mummunan barazanar kisa, sakamakon rikicin siyasa da kasar ta fada tun bayan da ya ba wa kansa cikakken iko.

https://p.dw.com/p/4DCMB
Tunesien Präsident Kais Saied
Hoto: Zoubeir Souissi/REUTERS

 Kakakin ma'aikatar cikin gidan Tunisiya Fadhila Khelifi ta ce hukumomi sun bankado wani shiri da ya kunshi bangarori na ciki da wajen kasar da ke barazana ga lafiyar shugaban kasar da kuma tsaron kasa da nufin haifar da hargitsi. Sai dai  shugaban gamayyar jam'iyyun adawa Ahmed Nejib Chebbi ya nuna shakku kan wannan sanarwa, inda ya ce wata dabara ce don gudanar da sabbin kame-kame da kuma daukar fansa kan abokan adawa.

Shugaba Saied na Tunisiya na shan suka daga bangaren 'yan adawa saboda mayar da su saniyar ware da ya yi a tattaunawar kasa kan sabon kundin tsarin mulkin da ake shirin kada kuri'ar raba gardama a kai a ranar 25 ga watan Yuli.  'Yan adawa da kungiyoyin kare hakkin bil'Adama na zarginsa da nuna son kai wajen samar da kundin tsarion mulki da ya yi daidai da muradansa.