1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Buhari ya gabatar da kasafin kudin 2021

Abdul-raheem Hassan
October 8, 2020

Gwamnatin Najeriya za ta kashe sama da triliyan 13 a sabon kasafin kudin badi, domin ceto koma bayan tattalin arzikin kasar saboda Corona da faduwar farashin mai.

https://p.dw.com/p/3jdyk
Muhammadu Buhari
Hoto: picture-alliance/dpa/M. Kappeler

Shugaban Najeriya Mohd Buhari ya gabatar wa majalisun dokokin kasar kasafin kudin shekarar 2021 a dai-dai loakcin da kasar ke fuskantar koma bayan tattalin arziki.

Shugaban ya gabatar da kasafin da ya kai naira triliyon 13.1, wanda ya zarta kasafin kudin bara da kashi 20 cikin dari. Shugaba Buhari ya ce kasafin kudin bana zai taimaka wa farfado da tattalin arzikin kasar.

Annobar Corona da rashin samun kudaden shiga da faduwar farashin danyen man fetur a duniya na daga cikin manyan matsaloli da suka nakasa tattalin arzikin Najeriya.