Shirin ya kunshi batun rashawar da ke kunshe cikin aikin yaki da corona a Najeriya, da batun sake mayar da Malam Abduljabbar na Kano gidan gyaran hali tare da bukatar likitoci su binciki lafiyar kwakwalwarsa. Akwai ganawa da aka yi tsakanin hukumomin Nijar da shugabannin kafafen watsa labarai masu zaman kansu.