A cikin shirin za a ji cewa a Najeriya, jami'an jinya da ke rasa rayukansu a sakamakon yaki da annobar corona na dada karuwa, lamarin da suka danganta da matsalar karancin kayan kare kai daga kamuwa da cutar a yayin da tarayyar Jamus ta zama abar koyi a duniya a fannin yaki da coronavirus.