Zaku ji yadda a Najeriya a yayin da kungiyar Boko Haram ke tsananta kai hare-haren a wuraren ibada da kasuwannni a sassan jihohin Arewa Maso Gabashin kasar, musulmi da Kirista sun dauki matakai na kare wuraren ibada daga irin wadan nan hare-hare da ke kara kamari la'akari da yadda mayakan kungiyar Boko Haram suka karkata wajen kai hare-haren kunar bakin wake a wuraren ibada a baya bayan.