A cikin shirin za a ji cewa yayin da ake ranar masu fama da cutar HIV mai karya garkuwar jikin bil adama, wasu dake dauke da cutar a Najeriya na sayar da maganin rage radadinta don sayen abincin da za su ci. A kasar Zimbabuwe kuwa, shugaban kasa Emmerson Mnangagwa ne ya soma fuskantar suka saboda nada wasu manyan sojojin kasar matsayin ministoci.