A cikin shirin bayan labaran duniya za ku ji tsadar kayan miya ta fara addabar magidanta a Najeriya. Akwai rahoto kan taron ECOWAS a Ghana game da yadda za a magance zullumin sake barkewar corona karo na biyu a Afirka ta Yamma da rahoto kan taron sasanci a Tunisiya game da samar da zaman lafiya mai dorewa a Libya. A Nijar kuma kungiyar daliban kasar ta kammala taron sasanci a cikin kungiyar.