A cikin shirin za a ji cewa, gwamnatin Najeriya ta sanar da kafa kwamiti na musanman don gudanar da bincike kan sace 'yan matan sakandaren Dapchi da ke a jahar Yobe na yankin arewa maso gabashin kasar, kamar yadda ministan yada labaran kasar Lai Mohammed ya sheda.